Isa ga babban shafi
Italiya

Firaminista Italiya ya nemi a mutunta hukuncin da kotu ta yankewa Berlusconi

Firaministan Kasar Italiya, Enrico Letta ya ce yakamata a mutunta hukuncin da kotu ta yankewa tsohon Firaminista Silvio Berlusconi, yayin da ake shirin kada kuri’a game da gwmnatinshi amincewa a yau.

Firaministan kasar Italiya, Enrico Letta
Firaministan kasar Italiya, Enrico Letta REUTERS/Remo Casilli
Talla

“A mulki irin na demokradiyya, ya kamata a zartar da kowane irin hukunci.” Inji Letta a lokacin da yake ganawa da ‘yan majalisar dattawan kasar.

Kuma bisa ga dukkan alamu wasu daga cikin ‘Yan Jam’iyar Silvio Berlusconi, za su bijire masa wajen goyan bayan gwamnatin kasar a kuri’ar amincewa da gwamnati da ake sa ran kadawa a yau, bayan ficewar wasu ‘Yan Majalisu daga gwamnatin hadin kai.

Angelino Alfano, mataimakin Berlusconi kuma Sakataren Jam’iyarsu, ya bukaci ‘Yan Majalisun Jam’iyar su da su goyi bayan Firaminista Enrico Letta.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.