Isa ga babban shafi
Italiya

An daga jirgin ruwan Concordia na kasar Italiya

Kusan shekaru biyu da yin hatsari, an daga jirgin ruwan Costa Concordia da ya fadi ta gefe a Tsibirin Giglio, a wani aikin ceto jirgin ruwa na farko da ya faru a duniya.

Jirgin ruwan Costa Concordia na kasar Italiya bayan an daga shi
Jirgin ruwan Costa Concordia na kasar Italiya bayan an daga shi REUTERS/Tony Gentile
Talla

An daga Concordia wanda ke da takun kafa 951 wanda kuma ke da nauyin tan 114,500 a cikin sa’o’i 19 inda masu kallo suka yi ta yin shewa bayan jirgin ya daidaitu akan ruwa.

Tun dai a watan Janairun shekarar 2012 gefen jirgin ke cikin ruwa bayan wani hatsari da ya yi lamarin day a yi sanadiyar mutuwar mutane 32.

Nick Sloane, wanda dan asalin kasar Afrika ta Kudu ne ya jagoranci aikin daga jirgin tare da hadin gwiwar wadanda suka gina shi.

“Wadanda suka gina jirgin sun taimaka matuka, tare da irin kayayyakin aikin da muke da shi, kuma da ba a samu hakan ba, da ba mu kai ga wannan shallin ba.” Inji Sloane, dan shekaru 52.

Hukmomin kasar Italiya sun ce yanzu za a ci gaba neman gawawwkin wadanda ba same sub a tun farko aukuwar lamarin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.