Isa ga babban shafi
Italiya

An kama wani Jirgin Ruwa makare da ‘yan gudun Hijirar Siriya da Masar.

A yau Juma’a Jami’an tsaron ruwan kasar Italiya sun sanar da cafke wani jirgin ruwa dauke da masu gudun hijra daga kasashen Syria da Masar, ciki har da yara kanana guda 31 da kuma mata 29. 

Wani jirgin ruwan kasar Australia
Wani jirgin ruwan kasar Australia REUTERS / AMSA /Handout
Talla

Hukumomin kasar sun bayyana cewa an kama jirgin ne wanda aka kera shi da katako a kusa da gabar ruwan garin Sicily dake Italiya.

Akalla ‘yan gudun hijra 5000 suka tsallaka zuw kasar ta Italiya daga Syria da Masar a cikin watannin uku da suka gabata.

Masu gadin gabar Ruwan Italiya sun bayyana cewar Direban daya auna tsawon Mita 5 kwatankwacin Kafa 49 domin kaucewa shiga Hannun Hukuma, ya shiga Hannu ne bayan da jami’an suka hango shi.

An dai bayyana cewar ya zuwa Watan Mayun wannan Shekarar ‘yan gudun Hijira kalilan ne ake samu daga wadannan kasashen, amma tsakanin Watannin Yuni da Yuli da Agusta an samu akalla ‘yan gudun Hijira Dubu Biyar 5.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.