Isa ga babban shafi
Syria

Daruruwan mutane sun mutu a harin da dakarun Syria suka kai a Damascus

Kungiyar kare hakkin bil’adama dake sa ido a rikicin Syria ta ce wani hari da dakarun kasar suka kai a sanyin safiyar yau a yankin Ghouta dake Damascus ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 100. 

Wani yanki da aka kai hare hare a Ghouta dake Damascus
Wani yanki da aka kai hare hare a Ghouta dake Damascus REUTERS/Mohamed Ibrahim/Shaam News Network/Handout via Reuters
Talla

Rahotanni na nuna cewa adadin mutanen da harin ya rutsa da su zai iya karuwa yayin da ake ci gaba da kai hare haren, inji kungiyar ta Syrian Observatory for Uman Rights.

“Adadin wadanda suka mutu zai iya karuwa, kuma ana ci gaba da kai hare haren.” Inji kungiyar wacce ta tattara bayananta daga ma’aikatan kiwon lafiyan kasar.

Sai dai kungiyar ba ta yi tsokaci game da zargin da ake yin a cewa dakarun sun yi amfani da makamai masu guba yayin da ‘yan tawayen kasar ke ikrarin mutane sama da 500 sun mutu ta dalilin hakan.

Gwamnatin kasar ta dai musanta hakan inda ta ce batun shaci fadi ne.

“Rahotanni dake nuna cewa an yi amfani da makamai masu guba a Ghouta babu gaskiya a ciki.” Hukumomin kasar suka bayyanawa kamfanin dillancin labaran kasar na SANA.

Zargin, a cewar gwamnatin kasar yunkuri ne na hana tawagar Majalisar Dinkin Duniya gudanar da ayyukanta na bincike game da yin amfani da makamai masu guba.

A jiya Talata ne tawagar Majalisar ta Dinkin Duniya ta fara gudanar da ayyukanta wanda jaridar Al –Watan ta ruwaito hukumomin kasar na ikrarin za su basu hadin kai dari bisa dari wajen gudanar da ayyukansu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.