Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai-Siriya

Kasashen Duniya sun dirar wa Siriya kan zargin amfani da Makami mai Guba, amma Rasha tace ba gaskiya ba ne

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya ce akwai kanshin gaskiya zargin da ake yiwa Gwamnatin Bashar Assad na yin amfani da makami mai guba kan masu adawa dashi.

Ma'aikatan Jinya a Siriya
Ma'aikatan Jinya a Siriya telegraph.co.uk
Talla

Wannan dai shine karo na farko da Shugaba Barack Obama ya fito fili yake tsokani gameda wannan zargi a tattaunawa da yayi da tashar TV ta CNN.

Itama dai kasar Burtania cewa tayi alhakin amfani da makamai mai guda na wuyan Shugaba Bashar al-Assad, kuma ya dace masu bincike daga MDD majalisar dunkin Duniya su hanzarta kutsa kai Syria domin karas da zargin da akeyi.

William Hague Sakataren waje na Britania yace dan tsakanin nan, kullun sai an sami sabon labari gameda zargin, saboda haka akwai bukatar yin wani abu cikin gaggawa.

Kungiyar Tarayyar Turai ma a ta Bakin jakadiyar Kungiyar Uwargida Cathrine Ashton cewa tayi bisa rahotanni da aka gabatar, akwai kwakkwarar shaida dake nuna anyi amfani da makamai masu guba a kasar Syria, kuma ya rage a dauki matakin daya dace.

Tace Kunghiyar kasashen Turai na goyon bayan kaddamar da cikakken binciken wannan zargi.

Gwamnatin Shugaban Syrian dai ta musanta wannan zargi da ake yi mata.

Ita ma dai kasar Russia yau ta sake fitowa fili tana cewa bata amince ba da dukkar wani kira na ayi amfani da karfin soji, wajen tursasawa Gwamnatin Syria.

Russia Tace bata goyi bayan dukkan take-taken afkawa kasar Syria ba saboda babu hujja.

Amma masu lura da al’amurra na kallon cewar zargin da kasashen yammacin Duniya ke yiwa shuga Bashar al-Assad na amfani da Makami mai Guba ga ‘yan kasar sa bai da tushe balle makama ganin cewar ai sun e ke taimakawa ‘yan tawaye da Makamai don yakar gwamnati.

Ana dai dari-darin cewar wannan maganar ta kasashen yammaci gaskiya ce saboda ba’a samu kara lalacewar wannan al’amari ba sai da Tawagar majalisar dunkin Duniya ta kai ziyara a Siriya, kuma ganin yanda shugaba Assad ke ci gaba da musanta wannan zargin, bai kamata a ci gaba da kakaba masa shi ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.