Isa ga babban shafi

Faransa ta kaddamar da shirin gaggawa na yaki da kwaron kudin cizo

Ma'aikatar Sufuri ta Faransa ta kaddamar da wani shiri na yaki da kwaron kudin cizo da aka fara gani kwanan nan a cikin motocin jama'a da gidajen sinima ko kuma gidajen kallo.

Kashi daya bisa goma na dukkanin gidajen da ke Faransa su na fama da wannan matsalar a cikin 'yan shekarun nan.
Kashi daya bisa goma na dukkanin gidajen da ke Faransa su na fama da wannan matsalar a cikin 'yan shekarun nan. AFP - JEWEL SAMAD
Talla

Matakan na zuwa ne a daidai lokacin da Faransa ke shirin karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon zari ruga ta Rugby, wanda ya jawo hankalin dubban masu ziyara zuwa kasar domin halartar gasar.

An gano wadannan kwarin a filin jirgin kasa da ke birnin Paris, da kuma filin jirgin sama na Charles-de-Gaulle, inda matafiya ke nuna kyama tare da yada faifan bidiyo a shafukan sada zumunta.

Ministan Sufuri, Clement Beaune, ya wallafa a shafinsa na X wato Twitter, cewa a mako mai zuwa za su sanar da matsaya kan matakan da aka dauka domin kare lafiyar matafiya.

Kwaron kudin cizon, wanda ya bace a shekarun 1950, ya sake dawo wa a cikin 'yan shekarun nan galibi saboda yawan  jama'a da karin zirga-zirgar su, inda suke buya a cikin katifa ko kuma tufafin kaya, yayin da suke fitowa cikin dare su na shan jinin mutane.

Gwamnatin Faransa ta bayar da kwangilar Inshora

Hukumomin kiwon lafiya na Faransa sun ce kwaron ya kasance babbar barazana ga lafiyar jama'a tun shekarar 2020.

An yi kiyasin cewa, kashi daya bisa goma na dukkanin gidajen da ke Faransa, su na fama da wannan matsalar a cikin 'yan shekarun nan, a cewar wani rahoto da hukumar kula da lafiyar jama'a ta Anses ta fitar a watan Yuli.

Don kawar da wadannan kwari, gwamnati ta ce ana bukatar bullo da wani tsari, wanda ke bukatar kusan Yuro 900 kuma zai kasance ana aiwatar da shi ne akai-akai

Hukumomin kiwon lafiya na Faransa sun ce kwaron a yanzu ya kasance barazana ga harkokin kiwon lafiya na kasar.

Zauren birnin Paris ya bukaci shugaba Emmanuel Macron, da ya taimaka wajen samar da shirin daukar matakin gaggawa yayin da Faransa ke shirin karbar bakuncin gasar Olympics a shekarar 2024.

Ina aka fi samun wadannan kwarin?

Hukumar kula da lafiya ta Faransa, ta ba da shawarar cewa mutane su duba gadajen otal yayin tafiya kuma su yi taka tsantsan game da shigo da kayayyakin da suka danganci katako ko kuma katifun da suke amfani da su.

Masana lafiya sun bayar da shawarar cewa, dole ne a yi amfani da maganin kashe kwari a dakunan da abin ya shafa cikin sauri.

Cizon kwaron yana haifar da borin jini, ko kuraje, kaikayi mai tsanani ko kuma haifar da rashin lafiya.

Har ila yau, sukan haifar da damuwa na tunani, matsalolin barci, da sauransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.