Isa ga babban shafi

Hukumar lafiya ta duniya ta yi gargadi akan matsalolin kiwon lafiya a DR Congo

Hukumar lafiya ta duniya ta magantu akan tabarbarewar lamuran lafiya a Jamhuriyar dimokaradiyar Congo, inda ta ce in ba a dauki matakan gaggawa matsalarfiya na iya haifar da munanan nakasa da kuma hasarar rayuka.

Harabar hedikwatar hukumar lafiya ta duniya WHO a birnin Geneva.
Harabar hedikwatar hukumar lafiya ta duniya WHO a birnin Geneva. © AFP
Talla

 

Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargadi akan tabarbarewar yanayin kiwon lafiya a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, inda kwalara, kyanda, mpox, anthrax da sauran annoba ke ragargazar al’uma.

Hukumar ta WHO ta ce Tashin hankali da tabarbarewar yanayi da gudun hijira talauci da kuma rashin abinci mai gina jiki na kara ta'azzara matsalar lafiya, sa’adda haka ta yi kira da a gaggauta samar da wadataccen kudi domin tunkarar lamuran.

Kalubalen da jama'ar DRC ke fuskanta sun kai wani mataki mai ban tsoro, in ji Boureima Hama Sambo, wakiliyar WHO a kasar.

A sassa da dama na kasar, musamman a gabashin DRC, fararen hula sun shiga wani mummunar matsalar lafiya da ta sake bulla kuma asibitoci sun cika makil da wadanda suka jikkata," kamar yadda jami'in hukumar ya shaida wa taron manema labarai a Geneva, ta hanyar bidiyo daga Kinshasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.