Isa ga babban shafi

Ma'aikatan lafiya sama da 4,000 suka bar Ghana zuwa aiki a kasashen Turai

Afirka – Akalla ma’aikatan kula lafiyar kasar Ghana da aka fi sani da nas-nas sama da 4,000 suka gudu daga kasar zuwa kasashen Turai da Amurka domin samun ayyukan da ake biyan albashi mai tsoka a wannan shekara, sabanin abin da ake biyan su a cikin gida, matsalar da ta haifar da karancin ma’aikata a asibitocin da ake da su a fadin kasar.

Wasu jami'an kiwon lafiya a kasar Ghana
Wasu jami'an kiwon lafiya a kasar Ghana AP - Sunday Alamba
Talla

Sakatare Janar na Kungiyar Nas-Nas da Unguwar Zoma a Ghana, Dr David Tenkorang-Twum ya ce tsakanin watan Janairu zuwa Yuli na wannan shekarar ta 2023, kusan nas-nas dubu 10 da 209 suka gabatar da bukatar samun takardar barin kasar saboda samun guraban ayyukan yi a kasashen ketare.

Jami’in ya ce daga cikin wannan adadi, kusan 4,000 sun samu takardar amincewa, kuma yanzu haka suna can inda suke aiki a kasashen waje.

Shugaban Ghana, Nana Akufo-Addo
Shugaban Ghana, Nana Akufo-Addo © RFI/France24
Shugabar Sashen Nas-Nas na babban asibitin Greater Accra, Gifty Aryee ta bayyana cewar ma’aikata 20 suka bar asibitin nasu zuwa Birtaniya da Amurka a cikin watanni 6 da suka gabata, yayin da asibitin Cape Coast ya ce ya yi asarar ma’aikata 22 da suka tsallaka zuwa Birtaniya, kamar yadda mataimakiyar shugabar sashen kula da nas-nas Caroline Agbodza ta tabbatar.

Jami’ar ta bayyana takaici a kan yadda kwararrun ma’aikatan su ke ficewa, yayin da matakin ke budewa wadanda suka rage kofar tafiya.

Ministan Lafiyar Ghana, Kwaku Agyemang Manu ya ce suna aiki tare da kungiyoyi cikin gida da na kasashen waje domin yadda za’a tinkari matsalar.

Manu ya kuma ce suna kuma aiki tare da ma’aikatar kwadago domin yi wa dokar Ghana gyaran fuska ta yadda za a takaita yadda ma’aikatan ke ficewa suna barin gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.