Isa ga babban shafi

WHO na zargin kamfanin India da zamba cikin aminci kan maganin tarin yara

Hukumar Lafiya ta duniya WHO da gwamnatin Gambia, sun zargi kamfanin harhada magungunan kasar India na 'Maiden Pharmaceuticals' da sauya samfuran magungunan tarin da aka mika wa masu bincike don tantance ko su ne sanadin mutuwar yara 70 a kasar Gambia.

Hedikwatar hukumar lafiya ta duniya a birnin Geneva da ke kasar  Switzerland.
Hedikwatar hukumar lafiya ta duniya a birnin Geneva da ke kasar Switzerland. REUTERS - Denis Balibouse
Talla

A cikin watan Oktoban shekarar 2022 ne gwamman yaran na Gambia suka rasa rayukansu, bayan shan maganin tarin kamfanin na India, wanda bayan gudanar da bincike hukumar WHO ta ce magungunan sun kunshi gubar da ta yi sanadin salwantar rayukan da dama.

A baya bayan nan ne dai wasu majiyoyi suka bankado zargin cewa, akwai wasu jami’an binciken na India da suka karbi cin hancin Rupee miliyan 50, kwatankwacin dalar Amurka dubu 600,000, inda suka sauya samfuran magungunan da za a bincika kafin mika su ga babban dakin binciken kasar, lamarin da ya sa sakamakon da aka fitar ya ci karo na da hukumar WHO.

Tun a karshen makon jiya ne dai, kamfanin na 'Maiden Pharmaceuticals' ya musanta zargin da ake masa na bayar da cin hanci don sauya bayanan magungunan tarin da suka yi sanadin mutuwar gwamman yara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.