Isa ga babban shafi

Akwai bukatar gwamnatocin Tarayyar Najeriya da na jihohi su karfafa yaki da cutar sankara

Masu ruwa da tsaki da ke fafutukar yaki da cutar sankara a Najeriya, sun yi kira ga gwamnatin kasar da na jihohi da su mayar da hankali wajen dakile yaduwar cutar sankara.

Parmi les 18 millions de nouveaux cancers diagnostiqués chaque année dans le monde, près de 3 millions sont causés directement par un microbe.
Parmi les 18 millions de nouveaux cancers diagnostiqués chaque année dans le monde, près de 3 millions sont causés directement par un microbe. © iStock - ClaudioVentrella
Talla

 

Sun yi wannan kiran ne a ranar Asabar 3 ga watan Fabrairu a Abuja yayin wani tattaki da wata kungiya mai fafutukar yaki da cutar sankarar Project Pink Blue ta shirya domin tunawa da ranar cutar ta duniya ta wannan shekara.

Masu ruwa da tsakin sun ce yin hakan zai taimaka wajen shawo kan matsalar cutar a kasar.

Shugaban tattakin kuma babban darakta na Project Pink Blue din Runcie Chidebe ya ce, “Muna barin dawainiyar maganin cutar kansa a hannun gwamnatin tarayya, amma muma muna da rawar takawa”.

Haka kuma akwai bukatar gwamnatocin jihohi su dauki mataki na kare al’ummarsu.

Ya ce rashin daukar matakin gaggawa wajen kula da cutar kansa shine babban abin damuwa a Najeriya, ya kara da cewa tsarin kiwon lafiyar kasar na bukatar gyara ta yadda za a taimaka wa marasa lafiya su kai kawunansu da wuri don gano cutar kansa da domin samun kulawa.

Ya kara da cewa akwai bukatar a kara yawan wuraren kula da lafiya a wasu domin rufe gibin kula da cutar kansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.