Isa ga babban shafi

Matasa sun zarta dattijai wajen kamuwa da cutar Cancer a duniya

Wasu alkaluma sun nuna karuwar matasan da ke kamuwa da cutar Cancer a sassan duniya, inda rahoton mujallar lafiya ta BMJ da ke bincike kan cutar ya bayyana cewa yanzu Cancer ta fi tsananta tsakanin ‘yan kasa da shekaru 50 sabanin a baya da aka fi ganin tsannatar tsakanin dattijai. 

Wani matashi da ya warke daga cutar Cancer
Wani matashi da ya warke daga cutar Cancer AP - Bilal Hussein
Talla

 

Rahoton da mujallar lafiya ta BMJ a Birtaniya mai bincike kan cutar Cancer ta fitar a wannan Laraba, ta ce har zuwa yanzu ba a kai ga gano ainahin dalilin da ke sanya karuwar matasan da ke kamuwa da cutar ta Cancer ba, amma binciken da ta gudanar ya nuna cewa tun daga shekarar 1990 zuwa 2019 alkaluman matasan da ke kamuwa da cutar ya karu da kashi 80. 

BMJ ta ce galibin masu kamuwa da cutar na tsakanin shekarun 14 zuwa 49 ne maimakon dattijai da a baya ke yawan kamuwa da cutar. 

Masana dai sun sanya cutar ta Cancer a sahun cutukan da suka fi addabar matasa ‘yan kasa da shekaru 50 a yanzu, wanda suka ce nada nasaba da karuwar yawan jama’ar duniya inda a bangare guda kuma wani rahoto na musamman ke alakanta hakan da rashin cin abinci mai gina jiki ko kuma abinci mai lafiya, baya ga karuwar zukar taba sigari da kuma kwankwadar barasa a matsayin manyan dalilan da ke haddasa cutar tsakanin matasa. 

Sai dai duk da wannan rahoto na masana, BMJ ta ce babu cikakken dalili a kimiyyance da ke bayyana dalilin karuwar matasan da ke kamuwa da cutar ta Cancer wadda ta kashe fiye da mutane miliyan guda ‘yan kasa da shekaru 50 daga 1990 zuwa 2019.  

Rahoton ya ce nau’in Cancer da suka fi kisa ga matasan sun kunshi sankarar mama da kansar makogwaro da ta hunhu da ta hanji baya ga ta ciki baki daya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.