Mahukunta sun kame gurbatattun kayayyaki na miliyoyin a jihar Neja
A kokarin kauda matsalar saida wa jama'a gurbatattun kayayyakin da suka tashi daga aiki, Hukumar da ke lura da ingancin kayayyaki ta Najeriya a jihar Neja, ta kai samame wasu kasuwanni da manyan rumbunan kayayyakin 'yan kasuwa da ma kantuna, inda ta kama tarin gurbatattun kayyaki da darajarsu ta kai miliyoyin naira.
Wallafawa ranar:
Kunna - 02:54
Wakilin RFI Isma'il Karatu Abdullahi ya bayyana cewa, kayayyakin da ta kaman sun hada da na abinci, lemu da dai sauransu.
Sayar da jabun magunguna a Najeriya ba sabon abu bane, abin da ke ci gaba da tayar da hankali hukumomi, musamman yadda jama'a ke yin gaban kai wajen sayen magani kai tsaye a kasuwanni ba tare da sahalewar likitoci.
Shiga alamar sauti, domin saurarin cikakken rahoton.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu