Isa ga babban shafi

Jérôme Salomon dan kasar Faransa ya shiga hukumar gudanarwa ta lafiya ta Duniya

Babban daraktan kiwon lafiya na Faransa, Farfesa Jérôme Salomon, ya shiga cikin tawagar gudanarwa na Hukumar Lafiya ta Duniya WHO a Geneva a yau Litinin, sanarwar da Majalisar Dinkin Duniya ta sanyawa hannu a hukumance.

Bafaranshe kwarrare a fanin kiwon lafiya Dokta  Jérôme Salomon,
Bafaranshe kwarrare a fanin kiwon lafiya Dokta Jérôme Salomon, AFP
Talla

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hukumar lafiya ta Duniya ta ayyana cewa wannan farfesa a fannin likitanci, wanda ya zama sananne ga Faransawa yayin annobar Covid-19, ya rike mukamin Mataimakin Darakta Janar na Kula da Lafiya ta Duniya da Cututtuka masu Yaduwa da Mara yaduwa. .

A cikin wannan tafiya, zai kula da babban sashen shirye-shiryen fasaha da sauransu da suka hada da  cututtukan da ake ɗauka ta hanyar jima'i, tarin fuka, zazzabin cizon sauro, al'amurran kiwon lafiya na tunani da cututtukan zuciya, ciwon sukari da ciwon daji.

Tedros Adhanom Ghebreyesus, Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya
Tedros Adhanom Ghebreyesus, Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya REUTERS - DENIS BALIBOUSE

Dokta Salomon, wanda ke da digirin a fannin ilimin cututtuka, ya riga ya kasance memba a hukumar gudanarwa ta WHO kafin nadin nasa kuma yana da "kwarewar a tsarin kula da lafiya, cututtuka masu yaduwa da lafiyar jama'a na kasa da kasa", in ji kungiyar.

Hukumar ta WHO ta nada jimillar sabbin mutane biyar ga tawagar gudanarwa a hedkwatarta da ke Geneva a yau litinin, wadanda tuni aka sanar da wasu daga cikinsu watannin da suka gabata. Wadannan nade-naden sun biyo bayan sake nada Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus a matsayin shugaban hukumar ta WHO a bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.