Isa ga babban shafi
Faransa-Lafiya

An yi wa dokar zubar da ciki gyaran fuska a Faransa

Majalisar Dokokin Faransa ta yi wa dokar zubar da ciki gyaran fuska, a daidai lokacin da ya rage kwanaki 46 a gudanar da zaben shugabancin kasar.

Mata na da damar zubar da cikin da bai wuce makwanni 14 ba a Faransa
Mata na da damar zubar da cikin da bai wuce makwanni 14 ba a Faransa REUTERS - EVELYN HOCKSTEIN
Talla

Majalisar dai ta amince da bai wa mata masu dauke da juna biyu damar zubar da ciki ko da kuwa ya kai makwanni 14 a maimakon 12 kamar dai yadda yake karkashin tsohuwar doka.

Wannan dai na nufin cewa cikin da bai wuce makwanni 14 ba, to ba laifi a zubar da shi a karkashin doka, kuma wadanda ke son yin hakan za su iya samun taimakon gwamnati.

‘Yan majalisa 135 ne suka amince da wannan sabuwar doka, 47 suka nuna rashin amincewarsu yayin da wasu 9 suka yi rowar kuri’unsu.

Ministan Kiwon Lafiya na kasar Olivier Veran, ya jinjina wa ‘yan majalisar a game da wannan sabuwar doka da ke tsawaita wa’adin zubar da ciki, yana mai cewa hakan gagarumar nasara ce a kokarin da ake yi na kyautata rayuwar mata a Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.