Isa ga babban shafi

Kasashen Afirka 12 zasu amfana da alluran rigakafin zazzabin cizon sauro

Kimanin allurai miliyan 18 na rigakafin cutar zazzabin cizon sauro na farko za a kai wa kasashen Afirka 12 nan da shekara ta 2025, in ji Hukumar Lafiya ta Duniya, UNICEF da Kungiyar Alurar riga kafi.

sauro nau'in Anopheles da ke haddasa kwayar cutar Malaria.
sauro nau'in Anopheles da ke haddasa kwayar cutar Malaria. © REUTERS/Jim Gathany/CDC/Handout via Reuters
Talla

 Shugaban hukumar lafiya ta Duniya  Tedros Adhanom Ghebreyesus ya shaida hakan a  wani taro da manema labarai cewa, "Malaria na daya daga cikin cututtukan da suka fi kashe mutane a Afirka, cutar na  kashe yara kusan rabin miliyan 'yan kasa da shekaru biyar a duk shekara."

A shekarar 2021, kashi 96 na mace-macen zazzabin cizon sauro a duniya ya faru ne a Afirka.

 An riga an bayar da  allurar rigakafin Mosquirix (RTS,S) da katafaren kamfanin harhada magunguna na Birtaniya GSK ya samar, ga yara sama da miliyan 1.7 a kasashen Afirka uku da suka hada da: Ghana, Kenya da Malawi.

Shugaban hukumar lafiya ta Duniya  Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce "An nuna cewa yana da aminci da inganci, hakan ya kuma taimaka wajen samu raguwar mutuwar yara.

Shugaban hukumar lafiya ta Duniya  Tedros Adhanom Ghebreyesus
Shugaban hukumar lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus © AFP

 Kusan kasashen Afirka 30 sun ce suna son a ba su allurai.

Baya ga kasashen uku da aka yi gwajin, wadanda za su ci gaba da karbar alluran rigakafi, wasu kasashe 9 ne za su ci gajiyar kayayyakin, in ji WHO, UNICEF da kuma kungiyar allurar rigakafi (Gavi).

 Kasashen sun hada da e Benin, Burkina Faso, Burundi, Kamaru, Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, Laberiya, Nijar, Saliyo da Uganda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.