Isa ga babban shafi

Hukumar NCDC a Najeriya ta ce mutane 798 sun kamu da cutar mashako

Hukumar da ke yaki da yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta tabbatar da barkewar annobar mashako, tana mai cewa a yanzu an tabbatar da kamuwar mutane 798 a sassan kasar.

Tabbarin hukumar da ke yaki da yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC.
Tabbarin hukumar da ke yaki da yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC. © Federal ministry of health
Talla

Ta cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce cikin mutane kusan 800 din da suka kamu, fiye da 654 na cikin wadanda suka ki karbar allurar rigakafin cutar.

Sanarwar ta ce jihar Kano ce ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar da mutanen 782 mafi yawan su kananan yara ‘yan shekaru 2-14, yayin da kaso 10 cikin wannan adadi suka rasa rayukan su a dalilin cutar.

Wannan dalili ya sanya hukumar ta NCDC ta ayyana barkewar cutar, tare da kira ga jama’ar kasar, da su dage wajen karbar rigakafin cutar musamman kan kananan yara ‘yan shekaru 15 zuwa kasa, saboda yadda cutar ta fi yi musu illa.

Wannan dai shine karo na biyu da cutar ke barkewa a Najeriya, bayan wadda ta faru a karshen shekarar da ta gabata, inda nan ma jihar Kano ta fi fama da yawan masu dauke da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.