Isa ga babban shafi

Yara miliyan 67 aka gaza yi wa rigakafi saboda annobar korona - MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin yara miliyan 67 ne suka gaza samun allurar rigakafin a sassan duniya tsakanin shekarun 2019 zuwa 2021, saboda kulle da aka tsaurara bayan bullar annobar Covid-19  da ta haifar da koma baya ga sha’anin kiwon lafiya ga kasashe, musamman matalauta.

Wasu iyalai kenan da ake yiwa yaransu rigakafin cutar shan inna a kasar Pakistan
Wasu iyalai kenan da ake yiwa yaransu rigakafin cutar shan inna a kasar Pakistan REUTERS/Fayaz Aziz
Talla

Fiye da shekaru goma na nasarorin da aka samu ga shirin rigakafin cutuka ga kananan yara sun samu koma baya mafi muni, a cewar wani rahoto da asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya fitar.

Daga cikin yara miliyan 67 da aka gazza cika musu sharuddan rigakafin, an samu miliyan 48 da ba a yiwa allurar ba, in ji UNICEF, abin da ya sa hukumar ta MDD nuna damuwa game da yiwuwar barkewar cutar shan inna da kyanda.

Yawan allurar rigakafi a tsakanin yara ya ragu a kasashe 112 kuma kashi 100 na yaran da aka yiwa allurar a duniya ya ragu da maki 5 zuwa kashi 81 cikin 100 da ba a taba ganin irinsa ba tun shekara ta 2008, inda tahoton ya ci gab adda cewa nahiyar Afirka da Kudancin Asiya ne suka fi fuskantar wannan matsala.

Alurar riga kafi na ceton rayukan yara miliyan 4.4 a kowace shekara, adadin da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar na iya haura miliyan 5.8 nan da shekarar 2030 idan an cimma burinta na barin babu kowa a baya.

Kafin bullo da maganin rigakafi a shekarar 1963, cutar kyanda na kashe kusan mutane miliyan 2.6 a kowace shekara, galibi kuma kananan yara, sai dai MDD ta ce, adadin ya ragu zuwa 128,000 a shekarar 2021.

Amma tsakanin shekarar 2019 zuwa 2021, yawan yaran da aka yiwa rigakafin cutar kyanda ya ragu daga kashi 86 zuwa kashi 81 cikin dari, kuma adadin wadanda suka kamu da cutar a shekarar 2022 ya ninka idan aka kwatanta da na 2021.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.