Isa ga babban shafi

Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin gwamnati da ma'aikatan jinya a Birtaniya

Ma'aikatan motar daukar marasa lafiya da ke yajin aiki a Ingila da Wales sun yi fitar dango ranar Laraba, lamarin da ya kara ta'azzara takaddamar albashi tsakanin gwamnati da dimbin ma'aikata.

Yadda ma'aikatan jinya suka gudanar da zanga-zanga a wajen asibitin St Thomas da ke birnin Landan ranar 20 ga watan Disambar 2022.
Yadda ma'aikatan jinya suka gudanar da zanga-zanga a wajen asibitin St Thomas da ke birnin Landan ranar 20 ga watan Disambar 2022. © NIKLAS HALLE'N / AFP
Talla

Yajin aikin ma’aikatan jinya ya haifar da zullumi a fadin Biritaniya, a daidai lokacin da ake shirye-shiryen bukukuwan Kirsimeti, inda ma'aikatan jirgin kasa da ma’aikatan shige-da-fice suka shirya kawo cikas ga bukukuwan hutu yayin da gwamnati ta sha alwashin kin amincewa da batun karin albashin.

Ma'aikata a Burtaniya dai na neman karin albashi shekaru da dama, inda yanzu haka kididdiga ta nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki ya kai kashi 11 cikin dari, abin da ya haifar da matsalar tsadar rayuwa mafi muni sama da shekaru goma.

Gwamnati da kungiyoyin kwadago sun yi ta muhawara kan yuwuwar asarar rayuka sakamakon yajin aikin, yayin da shugabannin hukumomin kiwon lafiya suka yi gargadi game da tabarbarewar harkokin kiwon lafiya.

A ranar Talata, dubban ma’aikatan kwalejin koyon aikin jinya da ke Ingila, Wales da Ireland ta Arewa ne suka gudanar da gangami, kwanaki biyar bayan yajin aikinsu na farko a tarihin kwalejin shekaru 106.

Duk da dagewar da gwamnati ta yi na cewa ba za ta tattauna da kungiyoyin kwadago ba, kuri'un jin ra’ayi da aka kadan sun nuna cewa galibin al'ummar birtaniya na goyon bayan ma'aikatan jinya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.