Isa ga babban shafi

Ma'aikatan jinya sun kara gudanar da yajin aikin gargadi a Birtaniya

Ma’aikatan jinya a Burtaniya sun gudanar da yajin aikin kwana guda karo na biyu kenan yayin da suke gargadin gwamnati game da karin albashi abin da masana ke ganin zai iya zama babbar illa ga harkokin kiwon lafiya.

Yadda ma'aikatan jinya suka gudanar da zanga-zanga a wajen asibitin St. Thomas da ke birnin Landan
Yadda ma'aikatan jinya suka gudanar da zanga-zanga a wajen asibitin St. Thomas da ke birnin Landan AP - Kin Cheung
Talla

Kimanin mambobi 100,000 ne daga Kwalejin koyon aikin jinya da ke Ingila da Wales da Ireland ta Arewa suka yi fitar dango karon farko a tarihin kungiyar na tsawon shekaru 106 a ranar Alhamis din da ta gabata.

Ma’aikatan jinya dai na bukatar a kara musu albashi mai tsoka, sakamakon hauhawar farashin kayayyakin da ake ci gaba da samu a kasar, amma gwamnati ta dage cewa ba za ta iya samar da wani abu ko da sama da kusan kashi 4-5 cikin dari ba.

Ma'aikatan jinya da ke yajin aiki na daga cikin yawancin ma'aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu a Burtaniya da ke daukar matakin yajin aiki kan albashi da yanayin aiki, yayin da suke fama da matsalar tsadar rayuwa da ta ta'azzara sakamakon hauhawar farashin kayayyaki shekaru da yawa.

Kididdigar farashin kayan masarufi a Burtaniya a halin yanzu ya kai kusan kashi 11 cikin dari, inda farashin makamashi ya yi tashin gwauron zabi bayan yakin Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.