Isa ga babban shafi
Mogadishu

Fararen hula 60 sun rasa rayukansu a Moghadishu

BARKEWAR wani sabon fada a birnin Mogadishu, dake kasar Somalia, yayi sanadiyar mutuwar mutane 29, daukacinsu kuma fararen hula.Ma’aikatan asibiti sun bayyana cewar, fadan ya barke ne da ranar jiya, inda akayi ta fafatawa cikin dare, tsakanin Yan kungiyar Al Shabaab, da kuma dakarun samar da zaman lafiya na kungiyar kasashen Afrika, bayan ta kaddamar dahari kan barikin soji.Ali Muse, jami’in kula da kwashe marasa lafiya a Moghadishu, yace ma’aikatansa sun kwashe mutanen da suka samu raunuka 98.A karshen makon da ya gabata ne, kaasr Uganda ta fara kai Karin dakaru 2,000 Somalia, dan karfafa wadanda ke aikin samar da zaman lafiya a cikin kasar. 

AFP / Abdurashid Abdulle
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.