Isa ga babban shafi

Wani sabon rikici a Habasha ya tilasta mutane dubu 50 barin matsugunansu

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane fiye da dubu 50 ne suka rasa muhallansu, sakamakon tashe-tashen hankulan da aka yi fama da su a yankin arewacin kasar Habasha, a dai dai lokacin da hukumomin kasa da kasa suka koka kan kazamin rikicin da ya sake barkewa a yankin, tsakanin ranakun 13 zuwa 14 ga watan da muke na Aprilu.

Yankin arewacin Tigray mai fama da rikici.
Yankin arewacin Tigray mai fama da rikici. © AP
Talla

Rahoton Majalisar Dinkin Duniyar ya ce yankunan da rikicin na baya bayan nan ya shafa sun hada da garuruwan Alamata da Raya Aalamata, da Zata da kuma Ofla.

Dukkanin garuruwan dai na a kudancin yankin Tigray ne, wanda ake takaddama kan mallakarsa, tsakanin shugabannin na Tigray da kuma mayakan yankin Amhara da suke makwabtaka da juna.

Bayanai na nuni da cewar tun bayan barkewar yakin Tigray tsakanin mayakan TPLF da dakarun gwamnatin Habasha a karshen shekarar 2022, mayakan yankin Amhara suka mamaye kudancin yankin na Tigray, inda suka dade suna ikirarin cewa dama nasu ne.

A baya bayan nan ne kuma mayakan na Amhara suka yi ƙorafin cewa yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla tsakanin gwamnatin Habasha da mayakan Tigray za ta rage musu karfin iko, la’akari da cewar yarjejeniyar sulhun ta bukaci ficewarsu daga kudan yankin na Tigray, inda a yanzu suke da iko, bayan da suka taimaka wa sojojin gwamnati wajen fatattakar mayakan TPLF da a baya suka nemi ballewa daga kasar ta Habasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.