Isa ga babban shafi
Zanga-Zanga

An yi zanga-zangar adawa da martanin Amurka kan rahoton kisa a Burkina Faso

Ɗaruruwan mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a wajen ofishin jakadancin Amurka a Ouagadougou, babban birnin Burkina Faso a jiya Juma’a, a game da martanin da Amurkar  ta yi a kan zargin da ƙungiyar kare hakkin ɗan adam ta  Human Rights Watch ta yi wa sojin ƙasar a nakisan fararen hula.

Wasu masu zanga-zanga a birnin Ouagadougou na Burkina Faso Burkina Faso. 16, ga Satumba  2015.
Wasu masu zanga-zanga a birnin Ouagadougou na Burkina Faso Burkina Faso. 16, ga Satumba 2015. REUTERS/Joe Penney
Talla

A wannan Litinin ce Birtaniya da Amurka suka bayyana matukar damuwa da takaici, kwanaki ƙalilan bayan da Human Rights Watch ta wallafa wani rahoto,inda take zargin sojin Burkina Faso da kisann fararen hula 223 cikin su har da yara ƙanana 56 a yayin harin martanin da ta kai kan wasu kauyuka biyu a rannar 25 ga watan Fabrairu.

Britaniya da Amurka  sun buƙaci Burkina Faso ta gudanar da bincike a kan lamarin, kana ta huƙunta wadanda suka aikata kashe-kashen.

Amma gwamnatin sojin Burkina Faso ta yi watsi da rahoton, tana mai bayyana shi a matsayin mara tushi ballantana makama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.