Mutane 9 sun mutu a harin da aka kai sansanin ƴan gudun hijira a gabashin Congo
Aƙalla mutanne 9, cikinsu yara ƙanana 7 ne aka kashe a wani harin bam da aka kai sansanin ƴan gudun hijira a birnin Goma na gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo a jiya Juma’a, kamar yadda kakakin sojin ƙasar da ma mahukuntan yankin suka tabbatar jim kaɗan bayan aukuwar lamarin.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Babu wani ƙarin bayani a game da irin bam ɗin da aka yi amfani da shi wajen kai harin, ko kuma wadanda ke da alhakin kai harin .
Hare-haren da ƙungiyar ƴan tawayen M23 mai samun goyon bayan Rwanda kai kaddamarwa tsawon shekaru 2 kenan yanzu ya fara karasawa birnin Goma a cikin ƴan watannin nan, lamarin da ya sa dubban mutane neman mafaka a cikin birnin.
Fadar gwamnatin Jamhuriyar Dinomakardiyar Congo ta bayyana a wata sanarwa cewa shugaba Felix Tshisekedi ya katse rangadin da ya ke yi a ƙasashen waje, inda ya yanke shawara dawowa gida a cikin ƙarshen mako.
Ba wannan ne karon farko da da ake kai hari kan sansanin ƴan gudun hijira a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, ko a cikin watn Yulin shekarar da ta gabata, sai da wasu mayaƙa suka kai hari kan wani sansanin ƴan gudun hijira a gabashin ƙasar.
Gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, na fama da kungiyoyi da dama masu dauke da makamai, tun bayan da rikici ya barke a kasar a shekarun 1990, inda yanzu haka masu bincike suka ce akwai irin wadannan ƙungiyoyi sama da 100 a yankin da rikici ke ci gaba da ƙamari.
Ƙasar ta jamhuriyyar demokradiyyar Congo ce ta fi kowacce yawan ‘ƴan gudun hijira a Afirka, inda Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa akalla mutane miliyan 5.6 ne suka kaurace wa gidajensu zuwa kasar sakamakon fadace-fadace.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu