Isa ga babban shafi

Harin M23 ya raunata dakarun MDD a Jamhuriyar Demokradiyar Congo

Wani sabon rikici da ya barke tsakanin sojojin jamhuriyar Demokradiyar Congo da ‘yan tawayen M23 ya raunata dakarun wanzar da zaman lafiya na Majlisar Dinkin Duniya a gabashin kasar mai fama da rikici.

Dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD MINUSCO a kudancin Demokradiyar Congo. 28/01/22
Dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD MINUSCO a kudancin Demokradiyar Congo. 28/01/22 AP - Moses Sawasawa
Talla

Babbar jami’ar tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Congo Bintou Keita da ta sanar da lamarin ta ce daya daga cikin dakarun wanzar da zaman lafiya ya samu mummunan rauni a harin da aka kai ranar Asabar.

Shaidu suka ce bayan dan kwanciyar hankali da aka samu, sabon rikici ya sake barkewa a gabashin Goma da ke lardin arewacin Kivu a ranar Asabar, sai dai kura ta sake lafawa da yammacin Lahadi.

Wani sojin gwamnatin Demokradiyar Congo ya shaidawa kamfanin dillacin Laran AFP cewar, jami’an na Majalisar Dinkin Duniya sun samu raunuka ne bayan rokokin da mayakan M23 suka harba ya fada cikin sansaninsu da ke Sake.

Rahotanni sun ce, mayakan M23 sun harba rokoki birnin ne, a matsayin martani kan harin da mayakan sakai na Wazalendo da ke goyon bayan sojojin gwamnati suka kai musu.

Kungiyar M23 da Tutsi ke jagoranta ta kaddamar da wani sabon farmaki makonni biyu da suka gabata a kan wasu garuruwa da ke da tazarar kilomita 70 daga Goma, inda ta fadada ikonta zuwa arewaci ta yankin Rutshuru da Masisi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.