Isa ga babban shafi

Ƙungiyoyin ƴan tawayen arewacin Mali sun kafa sabuwa haɗaka

Ƙungiyoyin ƴan tawaye da ke yaki da gwamnati a arewacin Mali sun ce sun kafa wata sabuwar haɗaka, inda suka naɗa wani jagoran ƴan ware a matsayin shugabansu, kamar yadda wata sanarwa da suka fitar ta bayyana.

Wasu daga cikin jagororin ƴan tawayen arewacin Mali.
Wasu daga cikin jagororin ƴan tawayen arewacin Mali. © AP
Talla

Sabuwar ƙwancen ta kare ƴancin al’ummar Azawad, wanda suka kira alliance, Permanent Strategic Framework for the Defence of the People of Azawad (CSP-DPA), zai kasance a ƙarƙashin jagorancin wani mai rajin neman ƴanci, Bilal Ag Acherif, kamar yadda wata sanarwa da ta fitar ya nuna.

 Acherif  dai dadadden mai adawa da gwamnatin Mali ne, kuma har gwamnatin ƙasar ta ƙaƙba masa takunkuman karayar tattalin arziki a watan Maris.

Biyo bayan wani taro na yini  5 da suka yi a ƙarshen watan Afrilu, waƙilan ƙungiyoyin Abzinawa sun sanar da kafa wani sabon tsari da zummar ci gaba da nema wa al’ummar yankin Azawad ƴancin su.

Azawad dai shine sunan yankin da ƴan awaren ke ikirarin cewa ƙasarsu ce a arewacn Mali, inda suke neman cin gashin kansu.

Ƙungiyoyin ƴan tawayen dai sun rasa iko da yankuna da dama a arewacin Mali a ƙarshen shekarar 2023, bayan wani samame da sojin Mali suka kai, wanda ya yi sanadin kwace yankin Kidal, inda  ƙungiyoyin ƴan aware suka fi ƙarfi.

Mali ta kasance a ƙasarkashin mulkin soji tun barin jerin juye-juyen mulki a shekarar 2020 da 2021, inda sojojin da suka ƙwace mulkin suka yanke hulɗa da tsohuwar uwargijiyar ƙasar, wato Faransa, suka kuma karkata zuwa Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.