Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 155 a Kenya
Firaministan Tanzania Kassim Majaliwa ya ce akalla mutane 155 suka rasa rayukansu a kasar, sakamakon mamakon ruwan sama da ake ganin ya haifar da ambaliyar ruwa da zamtarewar kasa.
Wallafawa ranar:
Firaministan ya ce sama da iyalai dubu dari biyu ne ambaliyar ruwar ta shafa, daga cikin adadadin mutane 155 sun mutu wasu 236 sun samu raunuka.
A lokacin da yake yiwa majalisar dokokin kasar jawabi a Alhamis din nan, Majaliwa ya ce bayaga asarar rayuka da ambaliyar ruwan ta haifar, ta kuma lalata gidaje da amfanin gona da hanyoyi da gadoji da layin godo da dai sauransu.
Yankin Gabashin Afrika na daga cikin yankunan da ke fama da matsalar sauyin yanayi wanda ya haifar da mamakon ruwan sama a daminar bana, inda ya haifar da asarar rayuka a kasashe irinsu Kenya da Burundi.
A Burundi, daya daga cin matalauciyar kasa a duniya, kimanin mutane dubu 96 ne ambaliyar ruwan ta raba da gidajensu, daga cikin wancan adadi mutane 45 ne kuma aka tabbatar da mutuwarsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu