Jam'iyyun siyasa na shirin kalubalantar Sojin Mali a gaban kotun kolin kasar
Kungiyoyin fararen hula da jam’iyyun siyasa a Mali sun bukaci kotun koli kan ta umarci gwamnatin sojin kasar da ta dakatar da haramcin da ta yi game da gudanar da harkokin siyasa.
Wallafawa ranar:
A wata sanarwa da suka fitar, kungiyoyin fararen hular da jam’iyyun siyasa da ke adawa da umarnin Sojojin, sun yi korafi ga babbar kotun kasar ta Mali, suna neman a soke hukuncin da suke ganin take hakkin Dan-Adam ne.
Tun a shekarar 2021 ne sojoji a Mali suka yi juyin mulki karo na biyu, inda suka yi alkawarin gudanar da zabe a watan Fabrairun daya gabata tare da maida mulki ga farar hula tun a watan Maris.
Sai dai mahukuntan kasar sun dage zaben a watan Satumbar bara saboda wasu dalilai, yayinda har zuwa yanzu basu sanar da dalilin gaza zaben na watan Maris ba.
Tashe-tashen hankula a kasar ta Mali na ci gaba karuwa, sakamakon gaza cika alkwarin gudanar da zabe da sojojin da ke mulkin kasar su ka yi a baya.
Lamarin da masu fafutuka ke kallon sa a matsayin koma baya ga dimokradiyya a kasashen yammaci da tsakiyar Afirka, inda aka yi juyin mulki takwas cikin shekaru hudu da suka gabata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu