Isa ga babban shafi

'Yan ta'adda sun kashe sojojin Nijar 23 a harin kwantan bauna

Karon farko tun bayan juyin mulkin Nijar a watan Yulin bara, gwamnatin Sojin kasar ta sanar da mutuwar dakarunta 23 a wani hari da ‘yan ta’adda suka kai musu a lokacin da suke tsaka da aiki a gab da iyakar kasar da makwabtanta Mali da Burkina Faso.

Wasu sojojin Nijar.
Wasu sojojin Nijar. AFP - ISSOUF SANOGO
Talla

A wata sanarwa da ba safai sojojin na Nijar suka saba fitar da makamanciyarta ba, ta ruwaito ma’aikatar tsaron kasar a jiya Alhamis na tabbatar da mutuwar sojojin 23 kan iyakar kasashen 3 a hare-haren ‘yan ta’addan na ranakun Talata da Laraba.

Duk da yadda Sojoji suka kwace mulkin kasar ta yankin Sahel a watan Yulin da ya gabata, hare-haren ‘yan ta’addan da kasar ke gani tsawon shekaru 8 daga kungiyoyi masu ikirarin jihadi na ci gaba da tsananta, duk da cewa Sojojin da ke mulki basu fiya bayyanawa ba face a wannan karon.

A cewar sanarwar ‘yan ta’addan su fiye da 100 sun yiwa Sojin na Nijar kwantan bauna ne a tsakar daji wanda ya kai ga musayar wuta tsakanin bangarorin biyu, kuma suma dakarun Sojin sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda akalla 30.

Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a tsakanin yankin Teguey da Bankilare inda ‘yan ta’addan suka dasa bama-baman gargajiya da kuma wasu motoci da suka ajje a hanya bama ɗana musu bam, lamarin da ya kai ga kisan Sojojin na Nijar 23 da kuma jikkata wasu 17.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.