Isa ga babban shafi

Juyin mulkin Nijar ya sake bai wa bakin haure damar kwarara Turai - EU

Kwamishiniyar harkokin cikin gidan kungiyar Tarayyar Turai Ylva Johansson, ta ce juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar a shekarar da ta gabata, ka iya haifar da karuwar kwararar bakin haure zuwa nahiyar, a daidai lokacin da ake shirin kada kuri'a kan yin garambawul ga dokokin 'yan cirani na kungiyar, gabanin zabenta a watan Yuni mai zuwa.

Kungiyar Tarayyar Turai ta ce juyin muliin Nijar ka iya haifar da kwararar bakin haure nahiyar.
Kungiyar Tarayyar Turai ta ce juyin muliin Nijar ka iya haifar da kwararar bakin haure nahiyar. © Johanna Geron / Reuters
Talla

Su dai sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun soke dokar da ta taimaka wajen rage kwararar bakin haure daga yammacin Afrika zuwa Turai, inda a yanzu kungiyar ta EU ke kokarin sake kulla alaka da kasar don rage tafiya ci rani ba bisa ka’ida ba.

Wasu alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewar, sama da mutane  dubu 45 da dari 5 ne suka tsallaka nahiyar ta haramtatciyar hanya a cikin wannan shekarar kadai, duk da dai adadin bai kai na shekarar 2015 ba, inda sama da mutane miliyan daya yawancinsu ‘yan gudun hijirar Syria ne suka shiga Turai.

Tun daga lokacin ne kuma kasashen 27 mambobin kungiyar suka matsa kaimi wajen rage yawan kwararar bakin haure daga yankin Gabas ta Tsakiya da kuma Afrika, ta hanyar tsaurara tsaro a iyakoki da kuma dokokin neman mafata a nahiyar baki daya.

A yau ne dai Majalisar Tarayyar Turai za ta kada kuri'ar karshe kan kan daftarin kudirin dokokin ‘yan cirani, wanda ya takaita lokutan tantance wa da hanyoyin neman mafaka, tare da ba da tallafi ga kasashe membobin kungiyar da ke fuskantar kalubalen ‘yan cirani.

Sai dai wannan kudirin dokar na fuskantar turjiya daga kungiyoyin farar hula 161 bayan da a jiya Talata suka yi kiran a yi watsi da shi, ganin yadda suka ce ya  keta hakki dan Adam.

Federica Toscano ta kungiyar  Save the Children Europe, ta ce dokar za ta shafi kananan yaran da ke tserewa yaki da kuma fuskantar karancin abinci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.