Isa ga babban shafi

Nijar ta fara tattaunawa da Amurka kan bukatar janye dakarunta daga kasar

An fara wata tattaunawa tsakanin wakilan Amurka da mahukuntan Jamhuriyyar Nijar a kokarin janye dakarun Washington da ke sansanonin Soji biyu a kasar ta yankin Sahel.

Sansanin Sojin Amurka da ke jamhuriyyar Nijar.
Sansanin Sojin Amurka da ke jamhuriyyar Nijar. AP - Carley Petesch
Talla

Kasashen biyu dukkaninsu sun tabbatar da faro tattaunawar a jiya Talata, wadda za ta kai ga cimma yarjejeniyar fara janye dakarun rukuni-rukuni.

Tun farko gwamnatin Sojin Nijar ce ta sanar da kawo karshen yarjejeniyar girke dakarun Sojin na Amurka a cikin kasar ta Sahel, dakarun da ke ikirarin samar da tsaro a yankin mai fama da hare-haren ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi.

Sakataren yada labaran ma’aikatar tsaron Amurka manjo janar Pat Ryder ya ce tabbas kasar ta fara tattaunawa da mahukuntan na Nijar dangane da bukatar da suka mika, kuma kowanne lokaci daga yanzu Pentagon za ta aike da wakilci daga babban sansanin sojinta na Afrika don shiga tattaunawar.

Babu dai tabbacin tsawon lokacin da wannan tattaunawa za ta dauka gabanin cimma matsayar janye dakarun, sai dai a baya-bayan nan ana ganin yadda al’ummar kasar ta yankin Sahel ke ci gaba da mabanbantan zanga-zangar bukatar ficewar dakarun na Amurka.

Sansanonin Sojin Amurkan biyu da ke Nijar ya shafe fiye da shekaru 10 ya na aikin yaki da hare-haren kungiyoyin ‘yan ta’adda na ISIS da Al Qaeda a kasashen yammacin Afrika, kuma janye dakarun kai tsaye zai dankwafar da wannan aiki.

A cewar Janar Ryder ko shakka babu Amurka za ta ci gaba da aiki da sauran abokanan huldarta da ke yankin na Sahel wajen tabbatar da wanzuwar yakinta na yaki da ta’addanci don tabbatar da tsaron yanki da kuma baiwa manufofin Washington kariya.

Ficewar dakarun na Amurka kai tsaye ana alakanta shi da shigar dakarun Sojin Rasha 100 cikin kasar ta Nijar a farkon watan nan, bayan yarjejeniya tsakanin kasar ta gabashin Turai da Niamey a batutuwan da suak shafi tsaro da tattalin arziki da kuma ilimi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.