Isa ga babban shafi

Sai yanzu Amurka ta tabbatar da juyin mulki da sojoji su ka yi a Nijar

A karon farko kasar Amurka ta bayyana kawar da shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed daga karaga a matsayin juyin mulki, inda ta sanar da katse tallafin dala miliyan 500 da take bai wa kasar a matsayin agaji saboda kawar da zababbiyar gwamnati. 

Shugaban kasar Amurka Joe Biden yayin ganawa da manema labarai a kasar Findland. 13/07/23
Shugaban kasar Amurka Joe Biden yayin ganawa da manema labarai a kasar Findland. 13/07/23 © 路透社图片
Talla

 

Wata sanarwar da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Matthew Miller ya yi ta bayyana cewar zasu mayar da wadannan kudaden tallafi ne kawai da zaran sojojin da suka yi juyin mulkin sun gaggauta mayar da gwamnatin farar hula da ta sahihiyar hanya. 

Jami’in ya bayyana cewar sun dauki wannan mataki ne bayan kwashe watanni biyu suna ta kokari ta bayan fage tare da kungiyar ECOWAS da kuma kasar Faransa wajen ganin an mayar da shugaba Bazoum Mohammed karagar mulki, amma kuma hakar su bata cimma ruwa ba.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken yayin ganawa da shugaban Mohamed Bazoum a Niamey. 16/03/23
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken yayin ganawa da shugaban Mohamed Bazoum a Niamey. 16/03/23 AP - Boureima Hama

 Miller ya ce sojojin da suka yi juyin mulkin a karkashin dokar ta bacin da suka kaddamar, ya dace su mayar da gwamnatin farar hula a tsakanin kwanaki 90 zuwa 120, amma kuma lura da yadda al’amura suke tafiya babu wata alama da ke nuna cewar sojojin na shirin yin haka. 

Katse tallafi

Jami’in ya ce a karkashin dokokin Amurka, tabbatar da juyin mulkin ya bukaci katse taimakon da suke bayarwa, saboda haka suka dakatar da tallafin dala miliyan 200 da kuma wasu kudade daga cikin dala miliyan 442 da aka warewa kasashen dake tasowa masu bunkasa dimokiradiya. 

Ta'addanci

Miller ya ce Amurka za ta bar sojojin akalla dubu guda dake aiki a Nijar, yayin da wani jami’i ya ce sojojin ba zasu ci gaba da horar da takwarorin su na Nijar ba, sai dai sanya ido akan ayyukan ‘yan ta’adda. 

Shugaban mulkin sojin Nijar Abdourahmane Tchiani tare da mukarrrabansa a birnin Yamai
Shugaban mulkin sojin Nijar Abdourahmane Tchiani tare da mukarrrabansa a birnin Yamai © REUTERS/Balima Boureima/File Photo

Amurkar ta ce zata ci gaba da tafiyar da sansanin ta dake Agadez wanda ake amfani da shi wajen kai hari da jirage masu sarrafa kan su

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.