Isa ga babban shafi

Chadi da Nijar na ƙarfafa dangartakar diflomasiyya da tsaro

Ministan tsaron kasar Chadi Dago Yacoub ya kai ziyarar aiki Nijar a ranar Talata, inda ya gana firaminista Ali Mahaman Lamine Zeine da kuma takwaransa na Nijar.

Tawagar Chadi ƙarkashin jagorancin ministan tsaro sun gana da Franministan Nijar Lamine Zaine a Yamai. 07/05/24
Tawagar Chadi ƙarkashin jagorancin ministan tsaro sun gana da Franministan Nijar Lamine Zaine a Yamai. 07/05/24 © CNSP
Talla

A tattaunawar da suka yi, kasashen biyu sun bayyana kyakyawar dangantakar hadin gwiwa tsakanin su musamman a fannin tsaro.

Tsaron kan iyakar da kuma mayar da wani gungun 'yan kasar Chadi zuwa Ndjamena na cikin batu da ya fi ɗaukar hankali a ziyarar.

Da yake tsokaci, Ministan Tsaron Nijar Salifou Mody ya nuna gamsuwarsa da yadda suke tafiyar da al'amuran tsaro a yankin tafkin Chadi, musamman ayyukan rundunar hadin gwiwa ta kasashen yankin.

Alakar Najeriya da Nijar

Duk da cewa Nijar ta janye sojojin ta cikin dakarun kasashen tafkin Chadi da ke yaki da Boko Haram tun bayan juyin mulkin watan Yulin 2023, masamman saboda kin amincewa ta yi wani duk alaƙar soji da Najeriya wadda ke jagorantar yakin.

Hakan dai na faruwa ne sakamakon tabarbarewar dangantakar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu makwabta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.