Sojojin Nijar 6 sun mutu a wani harin bam a yankin Inates da ke kusa da Mali
Rundunar sojin Nijar a wata sanarwa ta bayyana mutuwar sojoji 6 sakamakon wani harin bam a kusa da Mali, an kai musu hari ta sama.Majiyar ta bayyana cewa sojojin sun dawo daga aikin sintiri daga Inates’ bayan ta tsallake rijiya da baya a wata mahakar ma’adinan da ke kusa da kauyen Tingara dake kudu maso yammacin kasar.
Wallafawa ranar:
Rundunar ta karasa da cewa wasu sojoji sun jikkata kuma an kwashe su da jirgi mai saukar ungulu zuwa asibitin birnin Yamai.
Ma'aikatar ta kara da cewa sa ido ta sama ya ba da damar "gano 'yan ta'adda uku da ke da hannu" a cikin wannan aiki ta’addanci.
Ta kara da cewa, "An bi su zuwa wani yanki" inda suka hada da "kusan wasu masu hannu da shuni guda ashirin" sannan kuma an kai harin ta sama, wanda ya basu damar kashe wasu ‘yan ta’addan tare da lalata tarin makamai.
A cikin wannan tsari, an sake kai wani hari ta sama a kan "gungun 'yan ta'adda" a yankin Amalaoulaou na kasar Mali,hakan ya baiwa rundunar tsaron ta Nijar damar kashe ‘ ;yan ta’adda takwas.
Garin na Inates na cikin yankin Tillabéri, wanda ya zama maboyar mayakan masu ikirarin jihadi a yankin Sahel, ciki har da na kungiyar Da'esh a cikin babban yankin Sahara karkashin inuwar kungiyar Al-Qaeda.
A watan Disambar 2020 a Inates, an kashe sojojin Nijar 71 a wani hari da aka kai sansaninsu, wanda kungiyar Al-Qaeda ta dau alhaki.
Tun bayan fadawa karkashin ikon sojoji daga karshen watan Yulin 2023, kasar ta Nijar ke karkashin jagorancin sojoji da suka dau alkawali na ganin sun karfafa tsaro a karkashin hadin gwuiwar kungiyar AES da ta hada da Mali,Burkina Faso da kasar ta Nijar.
Duk da wannan kokari,ita ma kasar Nijar na fuskantar kalubale, a yankinta na kudu maso gabashin ta da Najeriya,inda wasu kungiyoyi ke ci gaba da garkuwa da kuma kisan mutanen a kauyuka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu