Nijar da Mali da Burkina sun kulla yarjejeniyar yaki da ta'addanci
Jagororin gwamnatin sojin kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar sun kulla wata yarjejeniyar yaki da ‘yan ta’addda masu ikirarin jihadi tare da samar da hadin-kai ta fanni siyasa a tsakaninsu a kokarin da suke na maido da matabar kasashensu.
Wallafawa ranar:
Dukkannin kasashen 3 sun fuskanci juyin mulki tun daga shekarar 2020, sakamakon matsalar tsaro da suka samo asali daga ayyukan ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi, wadanda suka taso daga arewacin Mali a shekarar 2012, kana daga bisani suka bazu zuwa Nijar da Burkina Faso.
Bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar ne kugiyar ECOWAS ta kakaba wa kasar takunkumai, bayan barazanar amfani da karfin soji da ta yi a kan masu juyi mulkin, tana mai bukatar maido da mulkin dimokaradiyya cikin hanzari.
Sakamakon haka ne a watan Satumba, Mali da Burkina da Nijar suka kulla kawance da zummmar taimaka wa juna ta bangaren soji idan batun kai wa wani daga cikinsu hari ya tabbata.
Juyin mulkin Mali da Jamhuriyar Nijar da Burkina sun haddasa lalacewar danngantaka tsakaninsu da tsohuwar uwargijiyarsu Faransa, inda suka karkata zuwa Rasha.
Sai dai a yayin da wannan sabuwar dangantaka da aka kulla ta ta’allaka ga tsaro ne kawai, shugaban mulkin sojin Burkina Faso, Kanar Ibrahim Traore ya ce ana iya fadadawa ta shafi tattalin arziki da sauransu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu