Isa ga babban shafi

Rashin adalci ke rura wutar ta'addanci a Afirka - Amina Mohammed

Afirka – Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci samar da wata cibiya a Afirka wadda zata mayar da hankali wajen tara bayanan asiri da musayar su a tsakanin kasashen dake yankin domin inganta yaki da ayyukan ta’addanci.

Taron yaki ta ta'addanci na kasashen Afirka
Taron yaki ta ta'addanci na kasashen Afirka © Nigeria presidency
Talla

Tinubu yace ya zama wajibi nahiyar Afirka ta shiga sahun gaba wajen yaki da ayyukan ta’addanci ta hanyar lalubo dalilan dake haifar da su, musamman wadanda suka hada da talauci da rashin daidaito da kuma rashin adalci a tsakanin al’umma.

Shugaban ya kuma ce, yayin da nahiyar ke wannan kokari, ya kuma zama wajibi a duba rassan ayyukan ta’addancin da suka hada da diyyar da ake biya da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, wadanda suke taimakawa sosai wajen samun kudaden da ‘yan ta’adda ke amfani da su.

Masu halartar taron yaki da ta'addanci a Afirka
Masu halartar taron yaki da ta'addanci a Afirka © Nigeria presidency

Tinubu yace bayan garkuwa da mutane da ‘yan ta’adda keyi, su kan kuma yi garkuwa da dukiyar al’umma ta biliyoyin daloli wadanda ya dace a yiwa jama’ar kasa aiki da su wajen basu ilimi, kula da lafiya da kuma samar da abinci, amma sai a dinga karkata su wajen aikata laifuffuka.

Shugaban yace kuskure ne yadda wasu jama’a ke cewa hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba bashi da nasaba da ayyukan ta’addanci, domin kuwa da irin wadannan kudade ake amfani da su wajen sayen makaman da ake aika aika da su.

Tinubu yace ya zama wajibi kasashen duniya su taimaka wajen dakile irin wadannan ayyukan ta’addancin wadanda ke yiwa nahiyar da duniya baki daya barazana.

Shugabannin Najeriya da Ghana da Jmahuriyar Benin
Shugabannin Najeriya da Ghana da Jmahuriyar Benin © Nigeria presidency

Shugaban taron, kuma mai bai wa shugaban kasar Najeriya shawara a kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana cewar matsaloli ne da dama ke ingiza ayyukan ta’addanci a Afirka da suka hada da manyan masu aikata laifuffuka da masu daukar nauyin ayyukan ta’addanci daga kasashen ketare da kuma basu horo da talauci da nuna banbanci a tsakanin al’umma da tashe tashen hankula da makamantan su.

Ribadu yace Najeriya ta tashi tsaye wajen tinkarar wadannan matsaloli, ciki harda masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, yayin da ta inganta hanyoyin tattara bayanan asiri da kuma tabbatar da hadin kai a tsakanin hukumomin tsaro tare da bai wa jama’a kwarin gwuiwa.

Mai bai wa shugaban shawara ya kuma bayyana shirin inganta bangaren shari’a domin hukunta wadanda aka samu da irin wadannan laifuffukan, yayin da ya kara da cewar gwamnatin Najeriya ta ci gaba da yiwa wadanda ake zargi da hannu a ayyukan boko haram shari’a.

Mataimakiyar Sakatare Janar ta Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed tace hanyar da za’a bi wajen yaki da ayyukan ta’addanci itace ta tabbatar da adalci a tsakanin jama’a da kuma jagoranci na gari.

Mohammed ta yi kiran mayar da hankali a kan illar da ayyukan ta’addanci ke yiwa ‘yam mata da mata tare da matasa, inda ta bukaci taimakawa wadanda ta’addanci ya shafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.