Isa ga babban shafi

Ƴan ta'adda sun kashe sojoji a jihar Neja

Allaka sojoji 6 da wani mafarauci sun rasa rayukansu yayin gwabza fada da ƴan bindiga a ungwannin Karaga da Rumace da ke garin Bassa a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja da ke arewacin Najeriya. 

Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya © Lekan Oyekanmi/AP
Talla

Rahotanni na cewa ƴan bindigan sun kuma kashe wasu manoma biyu, baya ga kona gidaje da babura da kuma rumbunan adana abinci.

Shaidu sun tabbatarwa manema labarai cewa da misalin karfe 9 na dare ne maharan suka farwa mazauna ungwannin, suka kuma share tsawon awanni suna abinda su ka ga dama. 

Shi ma Mustapha Bassa  ɗaya daga cikin shaidun da suka bayyana halin da aka shiga,  ya ce 'yan bindigan sun shiga ungwannin ne a kan babura, suna ta harbi babu kakkautawa.

Jaridar Daily trust a Najeriya, ta ruwaito an yi ta samun hare hare a baya bayan nan a ungwannin Allawa, da Bassa da kuma Madaka da ke kananan hukumomin Shiroro da Rafi a jihar Neja, inda aka kona kayakin abinci, da gidaje, da motoci da kuma wata kasuwa da darajar kayakin da ke cikinta ya kai miliyoyin naira. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.