An cika shekara guda da fara yakin kasar Sudan
Wallafawa ranar:
Kunna - 10:03
A farkon wannan makojn ne yakin da ake gwabzawa a Sudan tsakanin sojojin kasar karkashin Janar Abdel Fattah al-Burhan da kuma dakarun RSF da ke karkashin Mohamed Hamdan Dagalo ke cika shekara guda.
Rikicin da aka faro a ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2023, ya yi sanadiyar rasa rayuka da dama da kuma raba miliyoyi da muhallansu, wanda a yanzu MDD ta ce akwai barazanar barkewar yunwa a kasar.
Bangarori da dama ne dai suka yi yunkurin warware wannan rikici amma abin yaci tura.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Nasiru Sani.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu