Isa ga babban shafi
Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Kan halin rashin tsaron da arewa maso yammacin Najeriya ke ciki

Wallafawa ranar:

Wata kungiyar kare hakkin dan adam ta kasa da kasa da ake kira Global Rights ta bayyana cewa yankin arewa maso yammacin Najeriya shi ne mafi fuskantar ayyukan ta’addanci masu alaka da kashe-kashe ko garkuwa da mutane idan an kwatanta da yankin kudancin kasar.

Katsina na daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da matsalolin tsaro.
Katsina na daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da matsalolin tsaro. © Bashir/RFI
Talla

Rahoton da ya bayyana halin da ake ciki a yankin na arewa maso yammacin Najeriya da wani lamari mai tayar da hankali wanda kuma al’umma ba za su lamunci ci gaba da wanzuwarsa ba, ya ce wajibi ne mahukuntan kasar su lalubo hanyoyin warware matsalolin wannan yanki.

Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.