Isa ga babban shafi

Arewa maso yammacin Najeriya ya koma dandalin zubar da jini- Global Rights

Wata kungiyar kare hakkin dan adam ta kasa da kasa da ake kira Global Rights ta bayyana cewa yankin arewa maso yammacin Najeriya shi ne mafi fuskantar ayyukan ta’addanci masu alaka da kashe-kashe ko garkuwa da mutane idan an kwatanta da yankin kudancin kasar.

'Yan bindiga sun addabi wasu yankuna a jihohin Najeriya.
'Yan bindiga sun addabi wasu yankuna a jihohin Najeriya. © Leadership
Talla

Rahoton Global Rights da ya bayyana halin da ake ciki a yankin na arewa maso yammacin Najeriya da wani lamari mai tayar da hankali wanda kuma al’umma ba za su lamunci ci gaba da wanzuwarsa ba, ya ce wajibi ne mahukuntan kasar su lalubo hanyoyin warware matsalolin wannan yanki.

Manajan shirye-shirye na Global Right Mr Edosa Ovaiawe yayin wani taron zaman lafiyar yankin na arewa maso yammacin Najeriya da ya gudana a Abuja fadar gwamnatin kasar, ya ce cikin shekaru 10 da suka gabata, yankin wanda a baya ke sahun mafi samun kwanciyar hankali da zaman lafiya, ya juye zuwa mafi ganin ayyukan ta’addanci fiye da ko’ina a sassan kasar mafi yawan jama’a a Nahiyar Afrika.

Taken taron na jiya shi ne tabbatar a dorewar zaman lafiya da kawo karshen matsalolin tsaron da yankin ke fuskanta, rahoton na Global Rights ya ce matsaloli masu alaka da ayyukan ‘yan bindiga ya ta’azzara halin da yankin na arewa maso yammacin Najeriyar ke fuskanta na yawaitar kashe-kashe hatta a tsakanin tsirarun da ba ‘yan ta’adda ba.

Wasu fusatattun matasa bayan harin 'yan bindiga a Zamfara.
Wasu fusatattun matasa bayan harin 'yan bindiga a Zamfara. Dailytimes

Yayin taron na Talatar nan, mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3 da ya samu wakilcin Alhaji Sani Umar ya yi maraba da yunkurin Global Rights na horar da matan da suka fito daga yankin na arewa maso yammacin Najeriya don zama masu dogaro da kai da kuma shiga harkokin tafiyar da yankinsu, wanda ya ce zai taimaka matuka wajen magance matsalolin tsaron yankin.

Matsalolin tsaro a jihohin Zamfara da Kaduna da Katsina na ci gaba da lakume rayukan tarin mutanen da basu ji ba su gani ba, matsalolin da suka tsananta a shekarun baya-bayan nan tun bayan ta'azzarar ayyukan garkuwa da mutane don neman fansa.

Wasu daga cikin makaman da tubabbun Yan bindiga suka gabatar a Zamfara
Wasu daga cikin makaman da tubabbun Yan bindiga suka gabatar a Zamfara © Premium Times

Kawo yanzu yankuna da dama na wadannan jihohi basu iya zaunuwa bayan da al'ummominsu suka yi kaura don tsira da rayukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.