Isa ga babban shafi
Somaliya

Bam ya hallaka mutane shida a kasar Somaliya

Akalla mutane shida sun hallaka a Mogadishu babban birnin kasar Somaliya, sanadiyar tashin wani bam a gefen titi, kamar jami’ar da shaidun gani da ido suka tabbatar.An tayar da wannan bam cikin yankin kudancin birnin, kusa da wajen da jami’an tsaro ke wucewa, abunda yayi sanadiyar hallaka dakaru biyar daga cikin mutane shida da suka hallaka.Wani jami’in tsaron kasar ya shaida haka wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa, AFP, yayin da shaidun gani da ido suka tabbatar da mutuwar wata mata dake wucewa.Akwai wasu mutane masu yawa da suka jikata sakamakon wannan hari na ranar Laraba.

El ataque de los islamistas dejó una veintena de civiles muertos.
El ataque de los islamistas dejó una veintena de civiles muertos. ©Reuters/Feisal Omar
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.