Isa ga babban shafi
Afrika

Ci gaba da taro shugabannin a birnin Kampala

A ci gaba da zaman taronsu da suke yi a birnin kampala na kasar Uganda a jiya Litanin shugabannin kasashen nahiyar Afrika sun dauki niyar kara yawan dakaru a kasar Somaliya, domin yakar yan tsageran kungiyar alshabab, kamar yadda ministan harakokin wajen kasar Habasha (Ethiopia) Seyoum Mesfin ya sanar.A nasa bangaren ministan harakokin wajen kasar ta Somaliya Dehg Yusif yayi tsokaci dangane da halin rashin tsaro a kasar.Ya ce harakokin tsaro a kasar somaliya sun tabarbare tun da dadewa, wanda hakan kuma ya haifar da mummunan lamari ga al’umar kasar ta Somaliya da ma duniya baki daya, dan haka kasar Somaliya na bukatar taimakon gwamnatocin kasashen duniya, musamman na nahiyar Afrika wajen kawo karshen ayukan ta’addanci a cikinta.Shuwagabannin Kungiyar Tarayyar Afrika AU sun yi watsi da bukatar da kotun hukumta laifukan yaki ta Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta gabatar masu, na son buda wani reshenta a nahiyar Afrika.

Cérémonie d'ouverture du 15e sommet de l'Union africaine à Kampala, en Ouganda, le 25 juillet 2010.
Cérémonie d'ouverture du 15e sommet de l'Union africaine à Kampala, en Ouganda, le 25 juillet 2010. AFP/Marc Hofer
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.