François Hollande da wasu mutane daban sun bukaci a sako Marafa Hamidou Yaya
Tsohon sakatare janar na fadar shugaban kasar Kamaru Marafa Hamidou Yaya, wanda aka tsare da shi tun shekarar 2012 , dan siyasar mai shekaru 71, ya shigar da kira na neman ganin an sako shi sabili da yanayin lafiyarsa bayan ci gaba da tsare shi gidan kurkuku.
Wallafawa ranar:
Tsohon sakatare janar na fadar shugaban kasar ta Kamaru da aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 25 a gidan yari saboda samun sa da laifin almubazzaranci da kudin jama'a", ya shigar da wannan koke ne bayan da mujalar Jeune Afrique da ta samu hira da shi, ta kuma falasa halin da yake ciki a yanzu haka.
Kiran tsohon na hannun damar shugabar kasar ta Kamaru Marafa Hamidou Yaya ya shiga kunen wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a harkokin siyasar kasashen Duniya,inda tuni dai tsohon shugaban Faransa François Hollande da wasu mutanen daban suka yi kira da a sake shi saboda rashin lafiya.
Marafa Hamidou Yaya na fama da rashin gani ko cutar glaucoma, rahotani na bayyana cewa ya rasa amfani da idonsa na dama.
Marafa Hamidou Yaya ya na mai bayyana damuwa da gudu kada ya rasa idonsa daya cilo da ya rage,yayin wannan hira da mujalar ta Jeune Afrique ya ke mai bayyana cewa likitoci sun bayar da shawarar a yi masa tiyata wanda hakan zai ceto shi daga zama makaho.
Marafa Hamidou Yaya wanda ya ci gaba da bayyana damuwa ganin halin ko in kula daga Shugaban kasar ta Kamaru Paul Biya a wannan bukata ta shi, ya na mai shigar da wannan koke da cewa ya zuwa wannan lokaci,ba shi da masaniya bisa dalilan ci gaba da tsare shi da ake yanzu haka a gidan yari,a karshe ya na mai cewa wasu daga cikin mutane da aka kama shi da su a lokaci, an sake su a halin yanzu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu