Isa ga babban shafi
Somaliya

Sabon Fada ya hallaka mutane 24

Akalla mutane 24 suka hallaka sanadiyar fadan da ya barke a Mogadishu babban birnin kasar Somaliya, yayin da wani hari kusa da majalisar dokokin kasar.Kakakin majalisar dokokin Sheikh Aden Madobe ya shaida wa manema labarai cewa sun bukaci shugaban kasar, ya kafa sabuwar sabuwar gwamnati, bayan kada kuri’ar yanke kauna wa gwamnatin dake kan madafun iko.Amma Prime Minista Omar Abdirashid Sharmarke ya ce gwamnatin dake samun tallafin kasashen Yammacin Duniya zata ci gaba da aikinta. Sannan ya ce zasu ci gaba da gudanar da aikin hada kan kasa tare da neman mayar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar da ta shafe shekaru cikin yanayin yaki.Zaman majalisar dokokin kasar ta Somaliya na jiya Lahadi, shi ne na farka cikin wannan shekara ta 2010, amma kungiyar tawayen al-Shaabab da ake dangantawa da al-Qaeda ta kai hari da rokoki kan gidin majalisar, abun da ya janyo dakarun kiyaye zaman lafiya na kasashen Tarayyar Afrika mayar da martani. Akwai wasu mutanen masu yawa da suka jikata, bayan 24 da suka hallaka, yayin wannan farmakin.

Les troupes du gouvernement somalien et de l’Union africaine en mission en Somalie (Amisom) font face aux insurgés islamistes à Mogadiscio, le 11 mars 2010.
Les troupes du gouvernement somalien et de l’Union africaine en mission en Somalie (Amisom) font face aux insurgés islamistes à Mogadiscio, le 11 mars 2010. Reuters / Feisal Omar
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.