Isa ga babban shafi

Rabin 'yan ciranin Afrika na kaura ne a tsakanin kasashen nahiyar- Rahoto

Wani sabon rahoto da hukumar kula da kaurar baki ta Majalisar Dinkin Duniya IOM ta fitar ya gano yadda fiye da kashi 50 na ‘yan ciranin Afrika ke yada zango a tsakanin kasashen nahiyar don yin hada-hada maimakon tsallakawa nahiyoyin Turai da Amurka ko Asiya.

Wasu 'yan ciranin Afrika a Tunisia.
Wasu 'yan ciranin Afrika a Tunisia. AP - Hassene Dridi
Talla

Dai dai lokacin da kungiyar Tarayyar Afrika AU ke wani aikin hadaka da hukumar ta IOM wajen dakile yawan kaurar ‘yan ciranin na Afrika zuwa wasu nahiyoyi, kwatsam rahoton ya nuna yadda ‘yan ciranin ke karkata akalarsu safararsu a cikin nahiyar maimakon fita ketare.

Matsaloli masu alaka da tabarbarewar tsaro, rashin ingantaccen tsarin demokradiyya baya ga rikice-rikice da tashin hankali na matsayin manyan dalilan da ke haddasa yawaitar kaurar ‘yan ciranin na Afrika zuwa wasu sassa don tsira da rayukansu ko kuma samun ingantacciyar rayuwa.

Rahoton wanda ofishin IOM reshen Afrika ya fitar ya ce maimakon amannar da aka yi a baya na karuwar kaurar ‘yanciranin Afrikan zuwa Turai, lamarin ya sauya a yanzu ta hanyar da suke zabar kasashe tsakanin takwarorinsu na Afrika don zuwa yin cirani.

Mai magana da yawun ofishi na IOM a Afrika Yvonne Ndege ta shaidawa RFI cewa daga shekarar 2020 zuwa yanzu ‘yan ciranin na Afrika akalla miliyan 20 da dubu 800 ne suka yi kaura tsakanin kasashen nahiyar yayinda wasu miliyan 19 da dubu 700 suka tsallaka wasu nahiyoyi.

A cewar IOM wannan adadi na wakiltar kashi 51 cikin 100 na ‘yan ciranin da ke kaura a nahiyar Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.