Isa ga babban shafi
Premier League

Arsenal ta doke West Ham

Lukas Podolski da Olivier Giroud sun taimakawa Arsenal doke West Ham ci 3-1 a fafatawar da suka yi a jiya, wadanda suka zirara kwallayen a raga bayan West Ham ta fara jefa kwallo a ragar Arsenal. Arsenal tana fuskantar barazana ne daga Everton da ke neman haramta wa Arsene Wenger shiga gasar zakarun Turai a karon farko tsawon shekaru 17.

Tomas Rosicky ya rungume Olivier Giroud  wanda ya jefa wa Arsenal kwallo a ragar West Ham
Tomas Rosicky ya rungume Olivier Giroud wanda ya jefa wa Arsenal kwallo a ragar West Ham REUTERS/Eddie Keogh
Talla

Yanzu maki daya ne Arsenal ta ba Everton bayan ta hauro a matsayi na hudu a teburin Premier kafin Everton ta buga wasanta a yau da Crystal Palace.

A yau Laraba kuma Manchester zata yi fatar hucewa ne ne akan Sunderland bayan ta sha kashi a hannun Liverpool.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.