Arsenal zata yi kokarin shiga gasar zakarun Turai-Wenger
Arsene Wenger da ke horar da Kungiyar Arsenal ya amsa yana fuskantar barazana a kokarin samun hurumin jerin kungiyoyi hudu a teburin gasar Premier ta Ingila da zasu tsallake zuwa gasar zakarun Turai bayan Arsenal ta sha kashi ci hannun Everton ci 3-0 a Godison Park.
Wallafawa ranar:
Wenger ya sha alwashin tsallake wa zuwa gasar zakarun Turai.
Yanzu tazarar maki guda ne kacal ya raba Arsenal da ke matsayi na hudu a tebur da kuma Evaton da ke matsayi na biyar, kuma Evarton tana da kwanten wasa a hannu.
Karo 16 dai Arsenal na tsallakewa zuwa gasar zakarun Turai a jere, amma a bana Everton tana kokarin karya lagon na Arsenal.
Yanzu Liverpool ce a saman teburin Premier inda a karshen mako ta samu sa’ar West Ham ci 2 da 1.
Sau Tara a jere ke nan Liverpool ke samun nasara a wasanninta, kuma yanzu maki biyu ne tazara tsakaninta da Chelsea da ke matsayi na biyu.
A karshen mako nan mai zuwa, Manchester City da ke matsayi na uku, zata kai wa Liverpool ziyara, inda za’a iya tantance makomar Premier a karawar kungiyoyin biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu