Isa ga babban shafi
Champions League

Bayern da Atletico sun yi waje da Arsenal da Milan

Kungiyar Bayern Munich da Atletico Madrid sun tsallake zuwa zagayen Kwata Fainal bayan sun yi waje Kungiyar Arsenal da AC Milan A gasar cin Kofin zakarun Turai zagaye na biyu.

Dan wasan Bayern Munich Bastian Schweinsteiger a lokacin da ya zira kwallo a ragar Arsenal a gasar zakarun Turai a Jamus
Dan wasan Bayern Munich Bastian Schweinsteiger a lokacin da ya zira kwallo a ragar Arsenal a gasar zakarun Turai a Jamus REUTERS/Kai Pfaffenbach
Talla

Arsenal dai ta sha kashi ne a hannun Bayern Munich mai rike da kofin gasar da jimillar kwallaye ci 3-1.

A daren jiya an tashi wasa ne ci 1-1 a Allianz Arena, yayin da tun a Emirate Bayern Munich ta lallasa Arsenal ci 2-0.

Kokarin da Arsenal take yi na kawo karshen yunwar kofi, ga alamu yana neman ya gagari Arsene Wenger. Kodayake Arsenal ta tsallake zuwa zagayen dab da na karshe a gasar FA ta ingila amma tazarar maki 7 ne Chelsea ta ba Arsenal a teburin Premier.

A jiya Talata, Schweinsteiger ne ya fara zirawa Bayern Munich kwallo a raga daga bisani kuma Lukas Podolski ya rama wa Arsenal kwallon.

Bayan kammala wasan, Arsene Wenger ya dora laifin kashin da suka sha akan jan katin da aka ba dan wasan shi Wojciech Szczesny a karawa ta farko tare da sukar Arjen Robben dan wasan Bayern Munich da ya sa aka bayar da Jan katin .

Ko a bara a irin wannan lokacin ne Bayern Munich ta yi waje da Arsenal.

A daya bangaren kuma kungiyar Atletico Madrid ta lallasa AC Milan ne ci 4-1.

Wannan ne karon farko tun a shekarar 1997 da Atletico Madrid ta tsallake zuwa zagayen kwata Fainal a gasar bayan ta yi waje da AC Milan da jimillar kwallaye 5 da 1.

A yau Laraba ne kungiyar Manchester City zata kai wa Barcelona ziyara a Nou Camp inda City zata nemi rama kwallaye biyu da Barcelona ta zira a ragarta a Ingila.

A Faransa kuma Paris Saint-Germain ce zata karbi bakuncin Bayer Leverkusen wacce ta PSG ta cacccsa ci 4-0 a karawa ta farko a kasar Jamus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.