Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Sai mun ga bayan Leverkusen, inji Blanc na PSG

Mai horar da ‘yan wasan kungiyar Paris Saint Germaine na kasar Faransa, Laurent Blanc, ya ce ba za su zubar da makamansu ba duk da cewa sun yi nasara a kan Bayer Leverkusen a wasan farko a gasar zakarun nahiyar turai.  

'Yan wasan PSG na Faransa suna murnar zira kwallo a raga
'Yan wasan PSG na Faransa suna murnar zira kwallo a raga
Talla

A karawar farko da aka yi a Jamus, PSG ta doke Leverkusen da ci 4-0 inda a gobe Laraba kuma za a kara a zagaye na biyu a Faransa domin neman shiga zagaye quarter finals na gasar.

Sai dai masu sharhi kan kwallo kafa na cewa ba karamin jan aiki ba ne Leverkusen ta sauya sakamakon farko ganin cewa za ta kara ne a gidan PSG.
 

A yau Talata Arsenal za ta kara da Bayern Munich yayin da AC Milan ta kasar Italiya za ta fafata da Athletico Madrid.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.