Eto’o ya mayar wa Mourinho da martani
Samuel Eto’o ya mayar wa Mourinho da martani cikin raha da murmushi, yana mai cewa da tsufansa ya zirara kwallaye uku a ragar Manchester United a bana, bayan Kocin na Chelsea ya yi tsugumi akan shekarun Dan wasan na Kamaru da ya kafa tarihi a Turai.
Wallafawa ranar:
Eto’o yace idan har yana da shekaru 36 ko 37 zai iya zirara kwallaye uku a ragar Manchester, to hakan na nufin ko ya kai shekaru 50 yana iya cin kwallo a raga.
A ziyarar da Chelsea ta kai a Turkiya a gasar zakarun Turai, Mourinho ya fara amfani ne da Fernando Torres kafin daga bisani ya sako Eto’o
Torres ne ya fara zira kwallo a raga amma daga bisani Galatasaray ta barke kwallon, wanda hakan ke nuna har yanzu akwai rina a kaba a karawa ta biyu da za’a gudanar a Stamford Bridge, a Birtaniya.
Mourinho yace sun yi watsi da damar da suka samu bayan sun yi kunnen doki ci 1-1 da Galatasaray.
Kafar Telebijin din Canal Plus ce ta haska Mourinho yana fadar cewa Eto’o ya tsufa, yana mai bayyana shakku akan shekarun dan wasan ko sun haura 35 sabanin 32 a hukumance. Kuma Mourinho ya yi furucin ne a asirce kafin ya gana da manema labarai akan karawar Chelsea da Galatasaray.
Tuni dai Mourinho ya mayar da martani yana mai cewa ya fadi haka ne cikin raha a lokacin da ya ke kokarin bayani akan matsalolin Chelsea.
A lokacin da ya ke mayar da Martani Mourinho yace Eto’o dan wasan shi ne, domin ya horar da shi a Inter kafin ya dawo Chelsea.
Tun zuwa Samuel Eto’o Chelsea, kwallaye 8 ya zira a raga a haskawa 27, kuma Mourinho yana bayani ne akan matsalar Dan wasan gaba da ya ke bukata wanda ke cin kwallo a raga.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu