Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Mourinho ya yi tsegumi akan Eto'o

Kafin Chelsea ta fafata da Galatasaray a gasar zakarun Turai a gobe Laraba, wani batu da ya ja hankalin masoya kwallon kafa shi ne yadda wata kafar yada Labaran Telebijin a Faransa ta fallasa Mourinho yana tsegumi akan Samuel Eto’o ba tare da sanin ana daukar hotonsa ba.

Kocin Chelsea  José Mourinho yana shan hannu da Samuel Eto'o na Kamaru
Kocin Chelsea José Mourinho yana shan hannu da Samuel Eto'o na Kamaru REUTERS/Eddie Keogh
Talla

Kafar Telebijin din Canal Plus ce ta haska Mourinho yana fadar cewa Eto’o ya tsufa, yana mai bayyana shakku akan shekarun dan wasan ko sun haura 35 sabanin 32 a hukumance. Kuma Mourinho ya yi furucin ne a asirce kafin ya gana da manema labarai akan karawar Chelsea da Galatasaray.

Tuni dai Mourinho ya mayar da martani yana mai cewa ya fadi haka ne cikin raha a lokacin da yak e kokarin bayani akan matsalolin Chelsea.

A lokacin da ya ke mayar da Martani Mourinho yace Eto’o dan wasan shi ne, domin ya horar da shi a Inter kafin ya dawo Chelsea.

Tun zuwa Samuel Eto’o Chelsea, kwallaye 8 ya zira a raga a haskawa 27, kuma Mourinho yana bayani ne akan matsalar Dan wasan gaba da ya ke bukata wanda ke cin kwallo a raga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.